Babban kirarin da ake yi wa jam’iyyar APC na canji, hakika ya yi daidai da irin canjin da aka samu a cikin tafiyar jam’iyyar tun kafin ma ta cika shekara uku a kan mulki. A baya, kowane gurgu ko musakin dan siyasa, duk lankwashewar kafar sa, idan ya manna hoton sa da na Buhari, to ko bai yi kamfen ba, in dai an tsayar da shi takara, to ya ci ya gama.
Duk irin kuturtar dungulmin hannun dan siyasa da masu gyambo mai doyi a cikin su, muddun suka jingina da Buhari, to an daina kyamar su. Shi kan sa Buhari din tun farkon tafiya ya nuna cewa shi fa ‘inuwa ce, wadda ba ta kyamar kowa’, dalili kenan ma ya ce wa magoya bayan sa ‘a yi ‘SAK’ daga sama har kasa.
Tun tafiya ba ta yi nisa ba, sai APC ta fara sagada-sagada, ta yadda kowa ya fahinta cewa tafiya harkar fatauci a tsakanin kare da kura da bunsuru da rago tare, ba zai yiwu ba.
Al’amurra sun fara dagulewa yayin da zaben 2019 ke ta matsowa, yadda tuni shugabannin siyasa da masu rike da mukaman siyasa kowa ya kasa zaune ya kasa tsaye.
A na su bangaren, talakawan da aka ce don su aka kafa gwamnagtin APC tuni wasu sun zama hasalallu, har sun fara jifar wadanda suka jefa wa kuri’a tare da shan alwashin cewa a zaben 2019 ko Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba su umarni, to a wannan karon ba za su yi sak ba.
Shi kan sa Buhari din yanzu ta-kan sa ya ke yi, domin farin jinin sa a yankin Middle Belt ya ragu sosai, kamar yadda da yawa wadanda su ka yi ‘ko-Buhari-ko-a-mutu a Arewa, tuni tayar motar su ta sacce, ba su da wani katabus a yanzu.
Wani dalili da zai kara nuna wa mai nazari cewa da yawa sun hasala da mulkin APC ko rigingimun da ke cikin ta, shi ne wata kididdiga da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta fitar a cikin wannan satin. Kididdigar ta nuna cewa an fara sabunta katin rajistar zaben 2019 tun cikin watan Afrilu, 2017, wato shekara daya kenan cur. Amma daga cikinn jihohin da aka fi yin guguwar Buhari, jihar Kano ce kadai ke da yawan wadanda suka yanki katin zaben 2019.
Akasarin jihohin da aka fi yankar katin kada kuri’ar duk jihohin PDP ne, ko kuma a ce yankin Kudu-maso-gabas, yayin da sauran jihohi irin Lagos da Kano ke bin bayan su.
Ita kan ta Kano din bincike ya nuna cewa ‘mabiya darikar Kwankwasiyya ne suka fi yankar katin rajistar zaben 2019, su ma din da nufin huce-haushin yi wa Gwamna Abdullahi Ganduje ta-bare, ba don APC suka yanki rajistar ba. ‘‘Kwankwasiya a Kano mu ke, ba jam’iyya ba.” Haka Aminu Dumbulum, matashin mawakin Sanata Rabi’u Kwankwaso ke cewa a cikin wata sabuwar wakar Kwankwasiyya.
Ana cikin haka, sai APC ta shirya taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a cikin Fabrairu, 2018, inda maimakon a bayyana ranar da shugabannin jam’iyya na kasa, shiyya, jihohi da na kananan hukumomi za su sauka a sake zabe, tunda wa’adin sun a kusa da karewa, sai aka kara musu shekara daya.
DAUKAR DARASI DAGA PDP
APC ta yi tunanin kauce wa yin zabe ne, domin gudun kada garinn gyaran gantsarwa a kara kugu gaba daya. Sai dai kuma tuni wasu da hakan bai yi musu dadi ba, suka garzaya kotu, su na cewa an kauce wa ka’ida. To da farko me ya sa APC ta yi riga-malam-masallacin yin karin wa’adin?
Jawabin kara wa shugabannin jam’iyya na kasa da na jiha da kananan hukumomi wa’adi ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello. Sai dai kuma a gefe daya, yayin da wasu ke kallon cewa karin wa’adin da aka yi musu ya kauce ka’ida.
Wani abin dubawa kuma shi ne yadda aka fara taron aka gama aka bar Bola Tinubu da aikin sasanta bangarori masu rigingimu da junan su.Sai dai kuma karin wa’adin ya saukaka kunowar sabbin fitintinu da ka iya tasowa.
TSUGUNO BA TA KARE BA
Wata daya cur bayan kammala taron da aka kara wa shugabanni wa’adin shekara daya, sai APC ta kira wani taron, inda a yayin jawabin sa farkon wannan satin, Shugaba Muhammdu Buhari ya shammaci kowa, ya furta cewa wa’adin da aka kara wa shugabannin haramtacce ne, don haka a soke shi, su sauka a sake zabe. Canji dai sai kara canja launi ya ke yi, zuwa canje-canje.
DALILAN BUHARI NA A SOKE WA’ADIN
Shugaba Muhammadu Buhari ya jeron dalilai har 12 da y ace ya wajaba a soke wa’adin. Kadan daga cikin su y ace karin wa’adin ya kauce wa dokar jam’iyyar da kuma tsarin mulkin Najeriya. Sannan kuma ya ce duk wanda aka zaba a karkashin wannan lokaci na karin wa’adi, to muddin APC ta tsaida dan takara, ko ya ce zabe kotu kwacewa za ta yi.
Yayin da har yau babu wanda ya fito ya kalubalanci Buhari, a gefe daya kuma wadanda dama can karin wa’adin bai yi musu dadi ba, irin su Sanata Shehu Sani da babban jigon APC Bola Tinubu, sun fito sun yaba wa wannan shawara da Buhari ya bayar.
SANATA SHEHU SANI
“Ai da mun sake an tafi a cikin karin wa’adi har aka yi zaben-fitar-da-gwani, to da zaran wani dan adawa ya garzaya kotu, za mu iya wayar gari ga zabe ya zo, amma ba mu da dan takarar shugaban kasa, ‘yan takarar gwamnonin jihohi, na sanatoci da na majalisar tarayya. Domin ko da mun tsaida su, to kotu cewa za ta yi haramtattu ne, dama kuma haramtattun ne.”
“Wato abin da ke faruwa shi ne, akwai wasu gungun ‘yan-ta-kifen da ke yaudarar shugaban kasa da kuma jam’iyya, domin kawai neman biyan bukatar kawunan su. Dalili kenan kowa ya san tun da aka ci zaben 2015 jam’iyyar ta wargaje, hadin kai ya gagara, sabanin yadda aka san APC kafin a ci zabe.”
“Ni fa dama tun da aka yi wannan kasassabar na rika tunanin cewa, wai jam’iyyar da ta rika bin jama’a gida-gida ta na yi musu alkawurran kawo canji da kakkabe duk abin da ake yi ba bisa ka’ida ba, kuma wai aka wayi gari ita ce ta shimfida wannan haramtaccen karin wa’adin da babu shi a cikin dokar jam’iyya ko dokar kasa.”
“Wato akwai wasu mugaffalu a cikin jam’iyyar APC, musamman gwamnoni. A kowace Juma’a bini-bini za ka ga sun wanko riga sun je Sallar Juma’a a Fadar Shugaban Kasa. Su a na su tunanin jam’iyyar ta su ce, su kadai, domin sun fi kowa kusanci da shugaban kasa. Ba su komai sai faman fada da rikici tsakanin su da wadanda suka sadaukar da komai na su domin APC ta kafa gwamnati
“Tun bayan nasarar zaben 2015, sai daurin tsintsiyar APC ya faske, tsintsiya kuma ta tarwatse. Aka maida wasu mutane irin su Bola Tinubu, Bukola Saraki da sauran su saniyar-ware. Ba wai ina kwance wa junan mu zani a kasuwa ba ne, amma gaskiya ce na ke fada, kuma bayyana ta shi ne mafi dacewa.”
SANATA BOLA TINUBU
“Da Buhari ya ga dama sai ya kyale a tafi a karkace a kan tsarin da aka yi a karin wa’adi ga shugabannin jam’iyya a ranar 27 Ga Fabrairu, amma sai ya nuna shi mutum ne mai matukar ganin ya ja ragamar jam’iyyar nan zuwa ga hanya mikakka.
“Wannan rana abin farin ciki ce ga dukkanin masu so dimokradiyya tabbatacciya ta dore a kasar nan.
Tinubu ya kuma ci gaba da cewa abin da Buhari ya yi, zai kara karfafa jam’iyyar ta hanyar bayar da dama ga mambobin ta, ciki har da wadanda ke kan mulkin jam’iyyar a yanzu su wajen sake tsayawa takara domin su taimaka wa jam’iyyar kamar yadda su ke ganin ya dace.
Don haka sai ya kara da cewa ya kamata jam’iyyar ta hanzarta wajen shirye-shiryen gudanar da gangami da kuma zabukan sabbin shugabanni kamar yadda jadawalin zaben shugabannin jam’iyyar ya gindaya.
Ya ce wannan ba karamar nasara ba ce ga Najeriya baki daya, don haka ya kamata a yi watsi da tsohon salon siyasar dauri, a dauki sabon salo mai kara jaddada dimokradiyya da cikakkiyar dama ga kowa.
KOWA TA SA TA FISSHE SHI
Wannan kwatagwamgwama da ta dabaibaye jam’iyyar APC za ta iya kara damalmalewa idan har aka gudanar da zaben shugabannin da bai yi wa wasu dadi ba. Wasu za su iya canja jam’iyya yayin da wasu kuma za su hakura su zauna, amma ‘kadaran-kadahan, za su daina dukan jikin su da danyen kara saboda bauta wa APC.
Za a iya cewa idan aka sake zaben, to za a yi wa wasu gwamnoni ta-leko-ta-koma ne, domin tuni wasu jihohin har an gudanar zaben shugabannin jam’iyyu na kananan hukumomi, inda ake ta kukan cewa ba wasu wuraren ba zabe aka yi ba, dauki-dora dai aka yi.
Za a sa guyawun shugabannin jam’iyya na sama har kasa guyawunsu su yi sanyi, domin a baya har sun shantake cewa sai bayan an kallama zaben 2019 za su sauka. Kenan a yanzu za su zama yan kallo a harmagazar siyasa da kamfen na zaben 2019.
Talakawa kuma sun samu abin da suke so, saboda idan zabe ya zo, to kan su ya waye, sak ba za ta yi amfani ba. Yanzu dai sun koyi darasi kenan, kuma sun san “arna na boye sun gane na fili.” Kamar yadda mawaki Dauda Kahutu Rarara ya rika furtawa a cikin wata wakar sa a kamfen din 2015.
Shin ko dama ‘arnan siyasar’ a cikin APC su ke ne? Ji da gani da sauraren zuwan 2019 shi ne na mu.