Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, ya gargadi kasashen Afrika ciki har da Najeriya su yi kaffa-kaffa da gwamnatin Chana da kuma rikita-rikitar da ke tattare da sharuddan ciwo bashin kasar.
Tillerson ya yi gargadin cewa kasashen Afrika su rika jinjina nauyin bashi ko lamunin da Chana ke bayarwa, amma ba wai ya na kokarin raba kasashhen ba ne da huldar kasuwanci da Chana.
Ranar Alhamis Tillerson ya furta cewa Chana barazana ce ga ci gaban tattalin kasashen Afrika.
Ana ganin sakataren dai na kokari ne ya karkata hankalin nahiyar Afrika su maida hankali kan huldar cinikayya da Amurka, wadda ake yi wa kallon ta wulakanta nahiyar.