Najeriya ta rasa yara 800,000 saboda kin yi musu allurar rigakafi- Kamfanin GAVI

0

Shugaban kamfanin hada magugunan (GAVI) Seth Berkley ya bayyana cewa Najeriya ta rasa yara 800,000 sanadiyyar kamuwa da cututtuka a shekaru biyar da suke gabata.

Set ya ce an sami wannan yawa ne saboda rashin yi wa yara allurar rigakafin da ya kamata tun suna jarirai, da shina zai samar musu da kariya daga kamuwa da cututtuka.

” A dalilin haka ne kasar ke yawan samun bullowar cututtuka iri-iri kamar su cutar ‘Monkey Pox’, Bakon-dauro, Shawara, Sankarau, Zazzabin Lassa da sauran su.”

” Babu yadda za a yi gwamnatin kasar nan ta iya samun nasara wajen inganta kiwon lafiyar mutane idan har ba matsawa akayi da yi wa yara rigakafi ba kamar yadda ya kamata.

Bayan haka shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko Faisal Shuaib ya yi kira ga ma’aikatan da ke yi wa yara allurar rigakafi da su daina yin zuke a yawan yaran yaran da suka yi wa alluran. Ya ce lallai duk ma’aikacin da aka kama yana haka za a hukunta shi.

Ya ce daga yanzu hukumar za dauki mataki akan duk ma’aikacin da aka kama da laifin haka.

Daga karshe sarkin Suleja Muhammad-Awwal Ibrahim a madadin sarakunan gargajiya na jihar Neja ya yi alkawarin marawa gwamnati baya don ganin ta sami nasarar yi wa yara alluraar rigakafin.

Share.

game da Author