Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ta shaida wa gwamnatin Najeriya cewa idan har tana so ta cimma burin shirin Muradin karnin na shida a shekarar 2030 dole ne ta yi tanadin dala biliyan takwas domin samar wa mutanen kasar taftacaccen ruwan sha.
Jami’in asusun Zaid Jurgi ya bayyana cewa Najeriya za ta iya samar wa mutanen kasar tsaftattacen ruwa da muhalli ne idan ta ware wadannan kudaden sannan ta hada guiwa da kungiyoyi masu zaman kan su da asusun UNICEF.
Shirin Muradin karni na shida na nufin samar da tsaftattacen ruwa da muhalli wa kowa da kowa.