Mashahurin sarkin barkwancin nan a Najeriya, Atunyota Akpobome, wanda aka fi sani da Ali Baba, ya bayyana irin kuncin rayuwar da ya sha fama da ita kafin ya samu daukaka a fannin barkwanci.
Ya ce da wahala ta kai kamari, har kwandasta, wato karen-mota ya yi, domin rufa wa kai asiri.
Da ake hirar tambaya da amsa da shi a gidan talbijin na Channels, Ali Baba ya ce, “kai akwai fa lokacin da abubuwa suka kakare, sai na rika daukar motar mahaifi na ina yin taksi da ita. Haka na rika lodi ina jigilar fasinjoji daga tashar Ramah zuwa Ogbaazu cikin jihar Delta.”
“Idan na dauki motar mahaifi na na yi kabu-kabu da ita, to idan zan koma gida sai na sai masa tulin jaridu, na ajiye a kan teburin sa. Ta haka na ke rufe masa baki, ba ya yi min fada.”
Ya ce kuma ya yi aikin saukale da lodin barasa a wani kamfanin giya mallakar Alex Ibru, har sai da ta kai ma iyalan Ibru din sun san shi.
“To lokacin da na fara yin barkwanci a wurin biki, na je wani bikin iyalan Alex Ibru, sai wani daga cikin su ya ce min, “shin ba kai ne ka rika lodin katan-katan na barasa a masana’antar mu ba?” Na ce ‘ni ne.”
Ali Baba ya fara wasan barkwanci cikin 1988, shekaru 30 kenan da suka gabata.
Barkwancin sa da za a dade ba a manta ba, shi ne wanda ya kwaikwayi Patience Jonathan, uwargidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, dangane da katobarar da ta yi bayan an sace daliban Chibok.