Mutane uku sun rasa rayukan su a rikicin hako ma’adinai a Kaduna

0

Wani basarake a masarautar Kaninkon Yusuf Usman ya bayyana cewa mutane uku sun rasa rayukan su sanadiyyar barkewar rikici da aka yi a wurin hako ma’adinai dake Bakin Kogi a karamar hukumar Jema’a jihar Kaduna.

Usman ya fadi haka ne da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya ta yi hira da shi ranar Alhamis a Kafanchan.

Ya ce ricikin ta auku ne a tsakanin mazauna garin da wasu mutane da su ka zo domin hako ma’adinai ba tare da izini ba.

” Sanadiyyar wannan rikici mutane uku sun rasa rayukan su sannan hudu sun sami rauni wanda a yanzu haka suna samun kula a babbar asibitin Kafanchan.”

Share.

game da Author