Boko Haram sun kai wa wasu kauyukan karamar hukumar Madagali jihar Adamawa hari da daren Alhamis inda suka ji wa mutane da yawa rauni sannan suka sace mutane uku.
Mazaunan kauyukan Kaya da Milidu sun bayyana cewa Boko Haram sun kawo musu harin banzata ne sannan suka jidi abinci
a rumbunan su, kuma suka sace wasu ‘yan garuruwan su uku.
Da yawa sun tsira daga wannan hari ne bayan arcewa da suka cikin dazukan dake yankunan garuruwan.
Bayan haka shugaban karamar hukumar Madagali Muhammad Yusuf yace sakamakon fatattakar Boko Haram din ne da ‘yan farauta da ‘yan banga suka yi yasa basu aiwatar da abin da suka yi shirin yi ba, sannan Allah ya basu sa’a sun kashe wani dan Boko Haram daya.