Mutane da dama sun rasu a rikicin Makiyaya da Manoma a jihar Benuwai

0

Wasu mazaunan kauyen Omusu dake karamar hukumar Okpokwu jihar Benuwai sun sanar wa PREMIUM TIMES cewa akalla mutane 24 ne suka rasa rayukan su sannan mutane 20 sun bace sanadiyyar harin da wasu wanda ake zaton makiyaya ne su ka kai kauyukan su.

Wani mazaunin kauyen Omusu mai suna Attah Alexander ya bayyana cewa maharan sun far wa kauyen su ne da wasu kauyuka biyu (Okana da Okpilikpo) dake kwabtakata da su da misalin karfe 4 na yamma.

Alexander ya ce sanadiyyar hari da aka kai musu sama da mutane 2,000 sun zama ‘yan gudun hijira.

” Mun kirga gawan mutane 24 kuma mun kai mutanen da suka sami rauni asibiti da dama wanda mafi yawan su mata ne da yara kanana.”

Ya kara dacewa duk da zaman sojoji a garuruwan maharan sai da sukayi awoyi biyu suna ta’adi.

Ko da yake a wani rahoto da ya iske mu, ya bayyana cewa wasu kauyawa ne suka fara kai wa makiyaya hari inda suka illata mutane da yawa sannan suka sace daruruwan shanu.

Share.

game da Author