Kakakin rundunar ‘Operation Lafiya dole’ Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ta rasa dakarun ta biyu a arangama da suka yi da Boko Haram a dajin Sambisa dake Barno.
Nwachukwu ya ce duk da wannan hasara da suka yi na dakaru biyu, sun fatattaki Boko Haram, sannan sun kashe biyar daga cikin su.
” A ranar 28 ga watan Faburairu rundunar sojoji na ‘Operation Lafiya Dole’ sun fantsama wasu kusurwowin dajin Sambisa da ya hada da Agapulawa, Amuda, Nyawa da Attagara domin ci gaba da kakkabe sauran burbudin ‘yan Boko Haram. Dakarun sun kuma gano wasu maboyar Boko Haram a Tchikide da Chinene dake dajin Sambisa inda suka sami nasaran kashe biyar daga cikin ‘yan Boko Haram din.”