Musulmin kasar nan sun soki lamirin Hukumar Shirya Jarabawar Fita Sakandare (WAEC) kan yadda ta shirya za a rubuta wata jarabawar a daidai lokacin sallar Juma’a.
A cikin tantebur din jarabawar May/June 2018, an tsara daliban da za su rubuta jarabawar Chemistry cewa za su fara jarabawar ne da karfe 2 – zuwa 5 na yamma, a ranar 20 Ga Afrilu.
Ana gudanar da Sallar Juma’a tsakanin 1:30 zuwa 2:30 na rana.
Hukumar Shirya Jarabawar ta fito da jadawalin tantebur din tun cikin makon da ya bata domin ta zama kowane dalibi ya samu.
Za a fara jarabawar ranar 27 ga Maris, a kammala 15 Ga Mayu, 2018.
Shugaban Kungiyar Kare Hakkin Musulmi ta Najeriya, Ishaq Akinbola ya bayanna jadawalin jarabawar da cewa bai yi wa musulmi adalci ba.
Ya kuma kara cewa hakan na yin nuni da yadda ake tauye wa musulmi hakki da ‘yancin su a kasar nan.
“ Matsawar aka ce babu adalci, to zaman lafiya ba zai taba samuwa ba. Shi ya sa kowa ke ta hankoron a samu wanzar da zaman lafiya.”
Ya ce an dade WAEC na shirya jarabawar fita sakandare a lokacin sallar Juma’a, kuma musulmi sun sha ja wa masu shirya jarabawar kunne kamar a cikin 2016 da 2017.
“Amma gwamnati ta yi shiru, har sai musulmai sun fara dagula zaman jarabawar WAEC, har sai musulmi sun fara kekketa takardun jarabawar WAEC tukunna sannan gwamnatin tarayya za ta sa baki?”
“WAEC na sane ta ke wannan kuntatawa ga musulmi. So ta ke yi kawai kowace shekara musulmi su rika korafi. Shi ya sa su ke ta kokarin tunzura musulmi.”
Ya kara da cewa kuma hukumar WAEC a duk shekara ta na nuna kanta a matsayin cibiyar ilimi mai fada da adawa da musulmi.
“Tunda dokar Najeriya ta bai wa kowa damar yin addinin sa, to ita kuma WAEC tana yi wa musulunci zagon kasa ne wajen shirya jarabawa a lokacin da ake sallar Juma’a.
“Don haka mu na kira ga musulmai da ke kusanci da wurin rubuta jarabawa a lokacin sallar Juma’a, su hadu da wuri a inda za a yi jarabawar. Wannan kuma gargadi ne mu ke yi wa WAEC don kada ma ta sake ta yi wani abu.”
Shi ma Babban Limamin Jami’ar Fatakwal, Abdulrazak Kilani, ya bayanna cewa abin takaici ne a ce ko da yaushe sai musulmi sun fito su na karaji sannan za a ba su hakkin da ya wajaba a ba su a kasar nan.
Farfesa Kilani, ya ci gaba da cewa idan tafiya ta yi tafiya, to musulmin kasar nan za su nemi a maida Juma’a ta zama ranar hutu.
“Ranakun hutun Asabar da Lahadi duk Kiristanci ne. Amma awa biyun da musulmi ke nema a ba su domin su yi sallar Juma’a ana tauye musu ita. Tunda haka ne, ai sai musulmi mu nemi a ba mu Juma’a ta zama ranar hutu mu ma. Ai mu ma ya kamata a ba musulmi ranar hutun yin idabar mu.”
Wata lauya mai suna Mutiat Orolu-Balogun, ta ce ba daidai ba ne a rika shirya jarabawa a lokacin sallar Juma’a.
Da PREMIUM TIMES ta tuntubi WAEC, kakakin ta Demianus Ojijeogu, ya tabbatar da cewa za a yi jarabawar ‘Chemistry ta 1 da ta biyu da karfe 2 zuwa karfe 5 na yamma a ranar 20 Ga Afrilu, 2018. Amma ya ce hukumar ta tsara abin yadda ba zai zo daidai da lokacin sallar Juma’a ba.
Ya ce za a jinkirta jarabawar har sai wadanda suka tafi sallar Juma’a sun dawo.
“Za a jinkirta a kai 2:30, idan ta kama har 3 na yamma.”
Discussion about this post