1. Ina mai matukar farin cikin sake yi muku barka da zuwa wannan taro na Kwamitin Zartaswar mashahuriyar jam’iyya ta mu. Kamar yadda duk mu ka sani, Ina fatan za mu yi amfani da wannan taruwa da mu ka yi mu shawo kan wasu matsaloli sannan mu jaddada APC tare da kara mata karfin da za ta ci gaba da kare muradin jama’ar mu.
2. Musamman, ina ganin ya na da muhimmaci na yi jawabi na a takaice, a kan batun karin wa’adin da aka yi wa shugabannin jam’iyya na kasa da na jihohi. Kamar yadda muka sani, an gabatar da kudiri a taron mu na ranar 27 Ga Faburairu, 2018, inda aka amince da cewa idan wa’adin shugabancin su ya kare, to za su zarce su kara shekara daya cur.
3. Wannan kudiri ya samu karbuwa daga akasarin mabobin kwamitin mu, duk da cewa wasu mambobin jam’iyyar sun fito fili, sun nuna rashin amincewar su da tsarin. Kai, wasu ma har sun garzaya kotu sun ce ba su yarda ba.
4. To ni dai a nawa bangaren, na sake daukar lokaci na yi nazarin wannan hukunci da mu ka zartas. Kuma abin da na fahimta kuma na gano, shi ne, wannan hukunci ya kauce wa dokar jam’iyya da kuma dokar kasa baki daya.
5. Yayin da Dokar APC ta 17(1) da 13.2(B), ta takaita wa’adin shugabannin da aka zaba zuwa shekaru hudu, ta nuna cewa za su iya ci gaba amma tilas sai idan zaben kowanen su aka sake yi, sannan zai iya zarcewa. Ita ma Dokar Najeriya, wato tsarin mulki na 1999, wadda aka yi wa kwaskwarima, a cikin sashe na 223, ta nuna cewa shugabannin jam’iyyun siyasa tilas za su rika yin wa’adin shekaru hudu ne kawai, sai a sake zabe, kuma kada a sake a zarce shekaru hudun.
6. Sannan kuma , wani sashe na dokar jam’iyyar APC, an bayyana cewa shugabannin da ke son sake tsayawa takara tilas sai sun sauka daga mukaman su, akalla, wata daya kafin ranar sake zabe.
7. A kan haka ne, abin da ake bukatar gani daga gare mu, shi ne kawai mu shirya zabe sahihi da zarar wa’adin shugabannin yanzu ya kare. Maganar gaskiya itace, shugabannin riko ba za su iya magance wannan katankatana ba, kuma ba za su iya zama halastattu bisa ga wadanda za a zaba ba.
8. Sannan kuma ina ganin idan muka kauce wa wadannan sharudda da dokoki suka shimfida, to za mu jefa duk wata nasarar da jam’iyyar nan za ta samu a cikin barazana da hadari. Hakan kuwa na nufin cewa duk wani zaben fidda-gwanin da za su gudanar, to zai iya zama haramtacce.
9. Wannan fa ba a ma kai ga batun rarrabuwar kawunan da zai biyo baya ba, dama kuma kawunan jam’iyyar a rabe ya ke. Ko kuma na ce babu dankon siyasa mai zumunci a cikin jam’iyyar mu.
10. Don haka ina mai yakinin cewa zai fi kyau da alheri a bi tsarin da dokar jam’iyya da tsarin mulkin kasar nan ya shimfida, maimakon mu ja jam’iyyar mu mu afka cikin karankatakaliya.
11. Abin farin cikin ma shi ne har na amince da ranakun da aka aza za a yi tarukan gangamin jam’iyya da kuma zabukan shugabanni. Ina ganin hakan zai fi domin a samu wadanda za su ja mu ga samun gagarimar nasara.
12. Jama’a, ina kara yi muku barka da zuwa wannan taro, tare da fatan hakan zai kara karfafa mana kishin jam’iyya a zukatan mu.