Hukumar kula da aiyukan masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta janye masu yi wa kasa hidima dake aiki a wasu yankunan jihar Kaduna dake fama da rikici.
Jami’in hukumar Dahunsi Mohammed wanda ya sanar da haka ranar Laraba yace sun janye wadanda suka aika karamar hukumar Kajuru saboda rikicin da aka yi a Kasuwar Magani.
Ya ce za su dawo da masu yi wa kasa hidima karamar hukumar idan ta gamsu da yanayin tsaro a yankin.
Idan ba a manta ba a cikin watan Faburairu ne rikici ta barke a Kasuwar Magani dake karamar hukumar Kajuru inda akalla mutane 12 suka rasa rayukan su sannan aka kona gidaje da dama.
Wani mazaunin kauyen mai suna Yahaya ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an fara samun tashin hankula ne bayan wasu matasa sun ki yarda wasu ‘yan mata mazauna yankin su canza addinin da suke Kai zuwa wani addinin da bam.
” Ina mai tabbatar muku cewa wasu matasa sun bankawa shaguna da dama wuta a wannan kasuwar sannan mutane da dama sun sami raunuka kuma ni da idona na ga gawar mutum uku.”
Jim kadan bayan haka, gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya aika da Karin jami’an taro yankin sannan ya umurce su da su tabbata sun taso keyar duk wanda ya ke da hannun a wannan tabargaza.
Daga karshe gwamnan jihar ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar da ta kai kayan agaji yankin domin Tallafawa wadanda suka rasa dukiyoyin su a hargitsin.
Yanzu dai zaman lafiya a kankama a garin sai dai don a kiyaye tsautsayi ne hukumar ta ce sai ta tabbatar da yanayin tsaro tukuna kafin ta tura masu bautar kasar.
Discussion about this post