MU ZUBA MU GANI: Ko majalisa ta rattaba hannu a kudirin kafa Dakarun Zaman Lafiya, Buhari ba zai waiwaye ta ba

0

Wata majiya mai karfi daga Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa ko da Majalisar Tarayya ta rattabaa kudirin kafa Dakarun Zaman Lafiya, Buhari ba zai waiwaye ta ba.

A ranar Laraba Majalisar Wakila ta ce a shirye ta ke ta rattaba hannu a kudirin duk kuwa da cewa Buhari ya ki amincewa da saka hannu a kudirin don kafa rundunar.

Ita kuma gwamnati na kawo uzirin cewa babu wadatattun kudaden da za a rika kashewa wajen gudanar da ayyukn su ne babban dalilin da ya sa ba za ta iya kafa wannan hukuma ba. Sannan kuma akwai uzirin cewa duk wani aiki na tsaro da za a dauke su su yi, tuni akwai jami’an tsaron da ke yin aikin.

Don haka kamata ya yi a kara inganta wasu jami’ai na tsaro na ‘yan sanda da kudaden da za a kashe don kafa Dakarun Zaman Lafiya.

Shi kuma Shugaba Buhari ya ke amincewa kudirin ya zama doka tun cikin watan Fabrairu, inda ya kawo dalilan sa na kin amincewar.

“Su je din su saka hannu don kafa dokar su gni, ba wanda zai tsaida su ko ya hana su daga yin abin da su ka ga dama. Amma ko ka tilasta doki ka kai shi rafi, ai ba za ka iya tilasta shi ya sha ruwa ba.” Inji majiyarmu.

“In banda abin su, Shugaban Kasa ya ce babu kudin da za a kafa rundunar har a rika daukar dawainiyar ta. To idan Majalisar na da kudi aljihunta da za a iya daukar nauyin kafa ta, sai su maida himma.”

Share.

game da Author