MATSANANCIN YUNWA: An rasa yara 150 a jihar Gombe

0

Jami’in hukumar ciyar da yaran dake fama da matsanancin yunwa na jihar Gombe Suleiman Mamman ya bayyana cewa akalla yara 150 ne suka rasu a dalilin yunwa a shekarar 2017.

Ya fadi haka ne a lokacin da PREMIUM TIMES ta yi hira da shi a Gombe ranar Laraba.

Mamman ya ce a shekarar 2017 asibitocin jihar da ke kula da yaran dake fama da yunwa a kananan hukumomi hudu dake jihar sun karbi yara 14,143 inda daga ciki yara 13,069 sun warke bayan an basu magani da kula.

” Ko da yake mun yi iya kokarin mu wajen kula wa da wadannan yara da suka kamu da cututtuka ta hanyar aikawa da su wasu asibitocin domin su sami kulan da suke bukata amma duk da haka yaran basu tsira da rayukan su ba.”

Daga karshe kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kennedy Ishaya ya bayyana cewa jihar na daya daga cikin jihohi takawas da suka karbi bashin kudade daga babban bankin Najeriya don ganin sun kawar da wannan matsalar. Sannan ta mai da hankali wajen ganin ta kawo karshen wannan matsala.

Share.

game da Author