Matasa sun kona coci kurmus, sun cinna wa ofishin ‘yan sanda wuta a Kaduna

0

A yau Alhamis ne wasu matasa dake zama a unguwar Narayi, jihar Kaduna, suka kona cocin ‘Celestial Church’ kurmus sannan suka cinna wa ofishin ‘yan sandan dake unguwar wuta.

Kamar yadda bayanai game da wannan hargitsi ya iske PREMIUM TIMES, matasan sun kone cocin ne kan zargin da suka yi wa limamin cocin da kashe wani dan uwan su mai suna Sylvester Friday.

Matasan sun zargi Limamin cocin ne mai suna Steven Shittu da yin amfani da shi wannan dan uwa nasu wajen yin asiri, wato tsafi.

Hakan bai yi musu dadi ba inda suka yi ta fakon limamin amma basu sami sa’an kai ga shi ba.

Ganin yadda wadannan matasa ke ta kokarin daukan doka a hannun su ne ya sa jami’an ‘yan sanda suka boye shi.

Abin bai yi musu dadi ba, da asuban farko kuwa wato karfe 4 na safiyar Alhamis sai suka dunguma suka far wa cocin suka banka mata wuta sannan suka nufi caji ofis din dake unguwar ita ma suka cinnan mata wuta.

Ba a dai rasa rai ko daya ba a wannan hargitsi, inji Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi tir da wannan yamutsi da rashin hankali na matasan Narayi in da yace gwamnati za ta hukunta wadanda suka tada wannan hargitsi sannan ya umurci jami’an tsaro su gudanar da bincike kan mutuwar Sylvester.

Share.

game da Author