Wadanda suka yi garkuwa da Iyalan ma’aikacin Muryan Amurka ‘VOA’ Nasir Abdullahi Birnin – Yero sun sako su yau a Kaduna.
Masu garkuwan sun bukaci a biya su naira miliyan 12 kafin su saki maidakin sa da dansa da suka sace.
An biya masu garkuwan kudin fansar kafin suka saki su.
Idan ba a manta ba Birnin-Yero ya kokawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa wasu barayai sun yi garkuwa da matarsa ta dansa a gidan sa dake Birnin- Yero jihar Kaduna da misalin karfe 1:30 na dare.