Masu garkuwa sun bukaci naira miliyan 12 kudin fansar iyalan Nasir -Birnin Yero

0

Barayin da suka sace iyalen ma’aikacin ‘Voice of America (VOA) Nasir Birnin –Yero sun bukaci Naira miliyan 12 kudin fansar iyalan sa.

Masu garkuwan sun kira Nasir ne ta wayar selula, inda suka nemesa cewa ya kawo miliyan 12 domin fansar Iyalan sa.

Idan ba a manta ba Birnin-Yero ya sanarwa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa wasu barayai sun yi garkuwa da matarsa ta dansa a gidan sa dake Birnin- Yero jihar Kaduna da misalin karfe 1:30 na dare.

Wani daga cikin ‘yan uwan Nasir ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa masu garkuwan sun kira su ne jiya da safe.

” Ko da yake kudi fansar da masu garkuwan suka bukata na da dankaran yawa muna kokarin ganin iyalan dan uwana sun dawo gida lafiya.”

Share.

game da Author