Masari ya rantsar da sabon babban alkalin jihar

0

A yau Talata ne gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya rantsar da Musa Danladi a matsayin sabon babban alkalin jihar.

Masari ya rantsar da Danladi ne bayan ajiye aiki da tsahon alkalin jihar Abdullahi Yusuf ya yi.

Masari ya kwarzan ta Danladi cewa mutum ne mai kwazo da hazaka sannan ga mai da hankali wajen aikin sa.

Gwamnan ya yi kira ga sabon alkalin da ya maida hankali wajen ganin a gaggauta kammala kararrakin dake gaban kotunan jihar.

Share.

game da Author