Sanata Dino Melaye na jihar Kogi, ya bayyana wa Majalisar Dattawa yadda ya samu sa’ar yi wa zaratan ‘yan sandan SARS layar-zana a kotun Maitama, Abuja.
Jami’an tsaron dai sun yi masa kwanton-bauna ne a wajen kotun su na jiran ya fito su damke shi. PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito yadda ‘yan sandan suka ritsa shi har 7:30 na dare, shi kuma ya ki fitowa.
Da ya ke wa Majalisar Dattawa jawabi, Dino ya ce ya yi mamakin yadda jami’an tsaron suka kewaye kotun domin kawai su cafke shi.
“Ina cikin kotun aka tsegunta min cewa akwai ‘yan sandan rundunar SARS a waje su na zaman tsammanin jiran fitowa ta. Da na leko sai na gan su kusan 100. Kai ko cewa aka yi su je su kamo Shekau, to iyakar shirin da za su yi kenan.
“Ganin haka sai na ki fitowa, na koma neman mafita da kuma addu’o’i. To da ya ke ni dai na sa ubangiji na a gaba shi kadai, zan iya cewa mala’iku ne suka fice da ni, amma ba yin kaina ba ne. Don sai bayan da na fice da kamar awa biyu sannan suka gane ba na cikin harabar kotun.
“Gaskiya na yi mamakin yadda suka ritsa ni a kotu, a matsayi na na sanatan Najeriya, kuma wanda ya taimaki wannan jam’iyya ta mu ta kafa gwamnati, kamata ya yi idan su na nema na, sai su rubuto wa Shugaban Majalisar Dattawa, su shaida masa cewa ya sanar da ni ‘yan sanda na neman na bayyana a rana kaza.
An dai maka Dino Melaye ne kotu a ranar 1 Ga Maris, 2018, a bisa tuhumar sa da kazafi da kuma kantara wa jami’an ‘yan sanda karya cewa wani jami’in gwamnatin jihar Kogi ya kai masa hari da makamai da nufin zai kashe shi.
Sai bayan da yan sandan suka bincika, suka gano karya Dino ke yi.