Majalisar dokokin jihar Filato ta kafa wata kwamiti don samar mata da hanyoyin da za ta bi don iya kawo karshen tashi-tashinan da ake fama dashi a jihar Filato.
Majalisar ta amince da haka ne ranar Talata bayan Simon Kudu dake wakiltar Rukuba/Irigwe ya nemi majalisar ta yi hakan.
Kudu ya ce sanadiyyar rikice-rikicen, mutane da dama sun rasa rayukan su, wasu sun zama ‘yan gudun hijira sannan gidaje da dukiyoyi na miliyoyin naira sun salwanta.
Discussion about this post