A yau ne Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya yi sanarwar rufe majalisa a tafi hutun bukukuwan Easter.
Dama kuma gwamnatin tarayya ta sanar da ranakun Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutun bukukuwan Easter.
Ekweremadu ya yi addu’ar a yi bukukuwa lafiya, kuma ya kara da neman wa kasar nan zaman lafiya.
Za su koma bakin aiki a ranar 10 Ga Afrilu, 2019.
Majalisa dai ta fi kowane ma’aikaci a kasar nan saurin tafiya hutu da kuma dadewa kafin su dawo hutu.
Kada kuma a manta su na tafiya hutun shekara-shekara na wata daya.
Za a iya cewa wannan hutu ya zo wa majalisar faduwa ta zo daidai da zama kena, domin za a tafi hutun ne a daidai lokacin da aka fara caccakar su dangane da aringizon kudaden alawus-alawus da suke karba, yadda har an fara fitowa ana cewa kowanen su sai ya amayar da kudaden.
Discussion about this post