Majalisar Dattawa ta ki amince wa jihar Kaduna bashin dala miliyan 350

0

A yau ne majalisar dattawa taki amincewa da bashin dala miliyan 350 da gwamnatin jihar Kaduna ta ke nema bankin duniya ta bata domin gudanar da wasu ayyukan raya kasa da ta sa a gaba.

Wannan watsi da akayi da batun bashin ya biyo bayan mika rahoton kwamitin kula da basuka na majalisar dattawa wanda shugaban kwamitin Sananta Shehu Sani ya mika a gaban ta.

Ko da yake jajircewar hana wannan bashi da shugaban kwamitin majalisar ya mika na da nasaba da rikicin da ya turnike tsakanin sanata Shehu Sani da gwamnan jihar Nasir El-Rufai, kamar yadda masu sharhi suka bayyana.

Daya daga cikin dalilan da ya sa Shehu Sani ya ce ba zai amince wa Kaduna samun wannan kudade ba shine ganin cewa jihar Kaduna ce na biyu a jerin jihohin kasar nan da bashi yayi wa katutu.

Yace jihar Kaduna na da wadatar kudaden da take bukata domin gudanar da ayyukan ta ba tare da ta ciyo irin wannan dimbin bashi ba.

Sanatoci uku da ke wakiltar Kaduna duk sun ki amincewa da ba Kaduna wannan bashi. Da suke tofa albarkacin bakin su a zauran majalisar lokacin da ake muhawara a kai dukkan su sun ce ba za su amince wa jihar ta sami wannan bashi ba.

Sanata Suleiman Hunkuyi ya ce, abin da ya bashi mamaki a wannnan bashi da gwamna El-Rufai ya ke ta fadi cewa wai zai yi amfani da su shine, “ bayan mun duba dalilan da ya bada sai muka gano cewa ba haka bane, abinda ya rubuta da bam abin da yake ta fadi wa jama’a da bam.”

“ A matsayi na na mai wakiltar jama’a, wannan bashi bashi da amfani sannan bai kamaci jihar Kaduna ba domin nauyi ce kawai za a kara wa jihar.

Shima sanata Danjuma Lah, yace ba zai amince wa gwamna El-Rufai samun wannan bashi ba domin kuwa ba karbar bashin bane jama’arsa suka turo shi majalisa yayi.

Da ya nemi amincewar majalisar, mataimakin shugaban majalisar Ike Ekweremadu, ga ba dayan su sun ce basu amince a baiwa jihar Kaduna bashin ba.

Share.

game da Author