Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, ya nemi Majalisar Dattawa da ya gudanar da shiru na tsawon minti daya, domin girmamawa ga Marigayi Ali Wakili.
Wakili ya wakilci Shiyyar Bauchi ta Kudu ne kafin rasuwar sa ranar Asabar.
Daga nan kuma sai ya nemi Majalisa da ta dage zaman ta na yau Talata, kamar yadda ya ke al’ada a duk lokacin da wani mamba na majalisar ya mutu.
Daga nan sai Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya bada sanarwar dage zaman, kuma ya tunatar da su cewa ranar Laraba za a yi zama na musamman domin jimamin rashin marigayin tare da tuna kyawawan halayen sa nagari da kuma ayyukan alherin da ya shimfida.
Ya kuma kira ga Sanatoci kowa ya yi shiga ta kamala da mutunci a gobe Laraba.