Mahara sun kashe mutane 25 a jihar Filato

0

Wasu mahara sun kai hari wani kauye dake kusa da jihar Filato da jihar Kaduna ranar Litini inda mutane 25 suka rasa rayukan su a harin.

Bayanai sun nuna cewa kauyen da maharani suka kai hari na kusa ne da kananan hukumomin Kaura a jihar Kaduna da Bassa jihar Filato.

Wani mazaunin kauyen mai suna Timothy ya bayyana wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa maharan sun far wa kauyen ne basu san hawa ba, basu san sauka ba, sannan mutane 25 sun mutu a harin.

Rundunar ‘yan sandan jihar, sun fantsama domin farautar maharan.

Share.

game da Author