Likitocin jihar Kogi sun janye yajin aiki

0

A yau Talata ne kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Kogi (NMA) ta dakatar da yajin aikin da ta shiga da ya kai tsawon kwanki 72 a jihar.

Shugaban kungiyar Godwin Tijani ne ya sanar da wannan shawara da kungiyar ta dauka bayan ta kammala zaman gaggawa da ta yi a Lokoja.

Ya ce kungiyar ta amince ta dakatar da yajin aikin ne saboda rokon da shugaban kungiyar na kasa Mike Ogirima ya yi domin a sami damar sasantawa da gwamnati. Sannan da rokon da wasu likitoci suka yi saboda dangartakar dake tsakanin su da wasu marasa lafiya dake asibitocin jihar.

” Muna kira ga duk likitocin dake aiki a asibitocin gwamnatin jihar da su koma aiki daga ranar 22 ga watan Maris.”

Bukatun kungiyar sun hada da rashin biyan su likitoci albashi daidai da na kowa, rashin karin girma da sauran su.

Share.

game da Author