Kwannan nan za a ceto ‘yan matan sakandare na #Dapchi – Aisha Al-Hassan

0

Ministan harkokin mata Aishatu Alhassan ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokarin ganin an ceto ‘yan matan sakandare na #Dapchi da aka sace.

Aisha ta ce gwamnati ta aika da dakuru na musamman domin nemo inda aka boye wadannan ‘yan mata da zummar ganin an ceto su da ga hannun Boko Haram, sannan ta yi watsi da korefe korafen da ake ta yi wai gwamnati na nuna ‘halin ko in kula’ kan da sace ‘yan matan Dapchi din.

” Kamata ya yi mutane su gane cewa tashin hankali irin wannan na iya faruwa ga kowace gwamnati a duk fadin duniyar nan. Misali duk da irin ci gaba da kasar Amurika ta samu a fannonin fasaha da siyasa kasar bata rabu da harbe-harben bindogogi ba a makarantun kasar ba.

Ta roki jama’a da su taya gwamnati da addu’a sannan ta sanar cewa gwamnati ba za tayi kasa-kasa ba wajen ganin hakan bai faru ba.

Share.

game da Author