KWAMACALA: Ana neman Dino, An kori kwamishinan ‘yan sanda, Masu laifi sun gudu, Dino ya ba IG Awa 48

0

Jami’an tsaron sun bayyana cewa su na neman sa ne tare da Mohammed Audu, dan tsohon gwamnan jihar Kogi, Abubakar Audu

Jamai’an na ’yan sanda sun ce mutanen biyu da su ke nema, an sanar da ‘yan sandan kasa da kasa cewa da an gan su a damke su, saboda ana tuhumar su da laifin bayar da bayanan karya ga jami’an tsaro a wani bincike da Dino ya ce an yi kokarin kashe shi a cikin shekarar da ta gabata.

An dai gano daga baya cewa karya ce Dino ya yi wa wanda ya ce shi ne ya yi yunkurin kashe din.

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kogi, Ali Janga ne yayi sanarwar neman Sanata Dino da kan sa, kuma Hedikwatar Rundunar ‘Yan sanda ta watsa sanarwar a yau Laraba da rana.

Kafin hakan dai Melaye ya rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan sanda cewa zai kai kan sa kamar yadda aka bukata domin a bincike shi.

Amma kuma ya bayar da sharadin cewa zai mika kan sa idan a Abuja ne za a yi binciken ba a Lokoja, babban birnin jihar Kogi ba.

Ko a yau din nan sai da Melaye ya tashi a zauren majalisa ya yi wa ‘yan sanda tatas, ya na zargin su da hada baki kan makarkashiyar da ake yi kan sa.

WADANDA AKE TUHUMA TARE DA DINO SUN TSERE

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kogi ta bada sanarwar tserewar wasu masu laifin da ake tuhuma tare da Dino Melaye.

Wadanda ake tuhumar dai su na daga cikin wadanda aka kama da muggan makamai, kuma suka fallasa cewa Dino Melaye ne ke daukar nauyin su, kuma shi ya ba su makaman da kan sa. An kama su ne a cikin makon da ya gabata.

Sanarwar da aka fitar yau Laraba da safwe, ta ce wadanda ake neman bayan sun arce, su shida ne, wadanda su ka hada da: Kabiru Seidu, wanda aka fi sani da Osama, Nuhu Salisu, wanda aka fi sani da Small,sai kuma Aliyu Isa, Adams Suleiman, Emmanuel Audu da kuma Musa Mohmammed, wadanda suka arce daga inda ake tsare da su a Shiyyar A ta rundunar ‘yan sandan Lokoja.

Hudu daga cikin su dai alkali ne ya bada ajiyar su, cikin su hudun kuwa har da biyu da suka furta cewa Sanata Dino Melaye ne da Mohammed Audu ke ba su makamai.

Kwamishinan Yan sanda Ali janga, ya nuna fushi da takaicin tserewar wadanda ake tuhumar, tare da bada umarnin a kulle dukkan ‘yan sanda 16 masu tsaron inda wadanda suka tseren ke kulle.

DINO YA BA SUFETON ‘YAN SANDA AWA 48

Sanata Dino Melaye ya ba Sufeto Janar na ’Yan sanda awa 48 su kamo wadanda suka ce sun tsere, domin su bada shaidar da suka ce wai shi ne ya ke basu makamai ko kuma su hadu a Kotu.

Ya bayyana cewa tun farko dama ya ce sharri ne da rijiya ake neman a gina masa ya fada, kuma ake neman ganin bayan sa.

Ya ce tunda sun ce shi ne gogarman su, me ya sa za a bari su tsere.

SUFETON ‘YAN SANDA YA KORI KWAMISHINAN ‘YAN SANDAN JIHAR KOGI DA WASU MAN YAN JAMI’AN ‘YAN SANDA

Bayan tserewa da suka wadanda ke tsare a kurkuku dake jihar Kogi, sufeton ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris, ya kori kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi da wasu manyan ‘yan sanda dake jihar cewa sakacin da suka yi ya sa wadannan mutane suka tsere daga kurkuku.

Share.

game da Author