Sahihin labari daga Dapchi ya tabbatar da cewa maharan Boko Haram sun maida dalibai mata da suka sace daga Dapchi.
Ganau a garin ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa yau Laraba da sanyin safiya aka ga Boko Haram sun shigo garin Dapchi sun sauke daliban.
Shugaban Kungiyar iyayen da aka sace wa yara, Bashir Manzo, ya ce ya na Damaturu, amma zai garzaya zuwa Dapchi domin su kidaya su tabbatar da ko nawa ne aka maida.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ce a yanzu ya na kan hanyar komawa jihar Yobe daga Abuja.
Discussion about this post