Kungiyar likitocin Najeriya NMA ta kirkiro sabuwar baji don bambamta kawararrun likitoci da baragurbi a cikin su a kasar nan.
Shugaban kungiyar Mike Ogirima ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai, sannan ya kara da cewa kungiyar ta yi haka ne don gane wadanda suke bata aiyukan su a kasar nan.
Idan ba a manta ba a shekara 2017 ne Ogirima ya koka kan irin ta’adin da baragurbin likitoci yi wa aikin likitanci a kasar nan sannan da matsalolin da hakan kan jawo wa musamman marasa lafiya.
Domin kawar da irin haka ne ya sa kungiyar ta kirkiro sabuwar baji da duk likitan da ya yi rajista da kugiyar su zai dunga amfani da shi.
Ya kuma ce za a fara aiki da bajin a kasar daga ranar daya ga watan Afirilu sannan duk likitan da aka gano bashi da wannan baji za a dauke sa a matsayin baragurbin likita.