Kungiyar JOHESU ta ba gwamnati wa’adin kwanaki 30 ko ta fara yajin aiki

0

Kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya na JOHESU ta yi wa gwamnatin tarayya barazanar dakatar aiki nan da kwanaki 30 idan har ba ta biya mata bukatun ta ba.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa Ogbonna Chimela ne ya sanar da haka wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho ranar Laraba inda ya kara da cewa fannin kiwon lafiyar kasar za ta daina aiki dib idan har gwamnati bata biya bukatun kungiyar.

Idan ba a manta ba a watan Satumban 2017 ne kungiyar JOHESU ta janye yajin aikin kwanaki tara da ta yi saboda gwamanti ta tabbatar musu da cewa zata biya musu bukatunsu wanda ya hada da karin albashi, karin matsayi wa ma’aikata, gyara asibitoci da sauran su.

Chimela ya bayyana cewa yau watanni shida kenan gwamnati ta kasa cika wadannan alkawara da ta dauka.

” Tun a 2009 zuwa 2017 muke godo da gwamnati kan ta biya mana bukatun mu amma tayi watsi da mu.”

Ya ce ma’aikatan asibitocin gwamnatin tarayya za su fara shiga yajin aiki sannan ma’aikatan asibitocin jihar da ma’aikatan asibitocin kananan hukumomi su biyo baya.

Share.

game da Author