KUDIN MAKAMAI: An ba Dokpesi naira biliyan 2.1, ba aikin fari balle na baki -Jami’in Banki

0

Yayin da ake ci gaba da shari’ar Shugaban Kamfanin DAAR Communications PLC, Raymond Dokpesi, a gaban kotun Mai Shari’a John Dantsoho a Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, wani jami’in banki, kuma shaida, mai suna Abubakar Madaki, ya bayyana yadda Sambo Dasuki ya sa aka biya Dokpesi naira bilyan 2.1 ba tare da ya yi kwangilar ko sisi ba.

Ya ce kudin daga asusun Hukumar Tsaro ta Kasa aka cire su aka ba Dokpesi.

Madaki ya ce shi dai bai taba ganin kasafin Hukumar Tsaro ta NSA ba, ballantana ma a ce ya bi diddigin yadda aka kashe kudaden sa.

Ana tuhumar Dokpesi da kamfanin sa DAAR Communications masu gidan talbijin na AIT, a bisa laifuka shida na karbar naira biliyan 2.1 ba tare da ya yi aikin komai ba.

An dage shari’ar sai ranar 13 Ga Afrilu, 2018.

Share.

game da Author