KUDANCIN KADUNA: Gwamnati za ta gina wa wadanda suka rasa gidajen su a rikicin manoma da Makiyaya Sabbi

0

Gwamnatin tarayya za ta gina wa wadanda rikicin Makiyaya da Manoma ya shafa a kudancin Kaduna sabbin gidaje.

Babban Darekta a Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Kasa (NEMA) James Akujobi kuma jagoran kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin tantance irin ta’adin da akayi a rikicin ya bayyana haka a ziyarar da suka kai yankin.

Idan ba a manta ba mataimakin shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya fadi cewa gwamnati za ta taimaka wa mutanen da suka rasa gidajen su da dukiyoyin su a ziyarar da ya kai tun a wancan lokacin.

” Gwamnati a shirye take don ganin ta gaggauta gina gidajen da aka kona sannadiyyar rikicin saboda mutanen yankin musamman manoma cikin su su sami damar ci gaba da gudanar da harkokin rayuwar su.”

Bayan haka shugaban hukumar bada tallafi na gaggawa na jihar Kaduna (SEMA) Ben Kure ya tabbatar da cewa hukumar su zata mara wa kwamitin baya don ganin an gudanar da hakan.

Yayin da yake nashi tsokacin sarkin Kaninkon Tanko Tete ya yi maraba da aiyukan da kwamitin ta zo yi a yankin musamman yadda hakan ya nuna cewa gwamanti ta damu da halin da mutanen yankin ke ciki.

Kwamitin za ta ziyarci kauyukan kananan hukumomin Kaura, Jema’a da na Zangon Kataf.

Kauyukan sun hada da Ninte, Ungwan Ajo, Golkofa, Godogodo, Dogon Fili, Gadabiyu, Anton, Pasakori, Kario, Dalle, Asso, Goska, da Dangoma a karamar hukumar Jema’a.

Kauyukan Tachira, Tsonje, Adu, Tafan, Kukum Daji, Kukum Gida, Agban, A. A Abbas Filling Station, Takad, Garaje, Ashim, Mifi da Zilan a karamar hukumar hukumar Kaura.

Sannan kuma a Karamar hukumar Zangon Kataf akwai kauyukan Samaru Kataf, Katsit da Zonkwa. Karamar hukumar Kauru kuma akwai kauyukan Ungwan Magaji, Ungwan Rimi, Kaziti, Kigbeni da Kigam.

Share.

game da Author