Wata kotu a jihar Sokoto ta gurfanar da wani matashi mai suna Bilyaminu Sanusi dan shekara 25 mai sana’ar Welda kan yawan yi wa matan aure waya da daddare.
Lauyan da ya shigar da karar Umaru Rabiu ya bayyana cewa, Abdulkadir Ibrahim ya kawo karar Sanusi ofishin ‘yan sanda cewa yana yawan kiran matar sa da daddare.
” Abdulkadir ya fadi mana cewa Sanusi ya fara kiran matar sa ne tun a watan Janairun 2018 sannan duk kiran da ya yi mata sai ya tambayeta ko ta yi barci.”
Rabiu yace bayan ‘yan sandan sun gudanar da bincike a kan karar da Abdulkadir ya shigar sai suka gano cewa lallai lambar wayar da yake kiran matar tasa dashi ta Sanusi ce.
Ko da yake Sanusi ya karyata wannan batu cewa kazafi akeyi masa, alkalin kotun Abubakar Adamu ya bada belin sa kan Naira 100,000 tare da takardan shaidan biyan haraji a jihar, sannan ya daga ci gaba da shari’ar zuwa 10 ga watan Maris.