Ko kin san cewa yawan fushi ga mai ciki na cutar da kwanyar Jariri?

0

Wani likita a jami’ar Wayne dake Boston kasar Amurka, Moriah Thomason ya bayyana cewa yawan yin fushi ko kuma damuwa ga mai ciki na da matukar illa ga dan dake cikin ta domin hakan na hana kwakwalwar dan yin girma yadda ya kamata.

Thomason ya gano haka ne a binciken da ya gudanar kan yanayin girman jaririn dake cikin uwayen su.

” A shekarun baya idan ba a manta ba wasu likitoci sun bayyana illolin dake tattare da fushi ko damuwa ga mai ciki amma tun da basu tabbatar da haka ba mafi yawan mutane sun dauka canfi ne wanda ya sa na gudanar da wannan bincike don gano ainihin gaskiyar maganar.”

Ya ce ya gudanar da binciken ne kan wasu mata 47 masu cikin wata takwas da wata tara sannan ya zabo su daga wureren da mutane suka fi fama da matsalolin halin rayuwa.

Thomason yace binciken ya nuna cewa sanadiyyar damuwa na halin rayuwar yau da kulum da yawan fushi da wadannan mata ke fama da su ya hana kwanyar ‘ya’yan dake cikin su yin girma yadda ya kamata.

A dalilin haka yake kira ga mata musamman masu ciki da su yi kokari su rage yawan damuwa da yin fushi domin guje wa haiho musakan ‘ya’ya.

Share.

game da Author