Wata matar aure mai shekaru 35 Bilikisu Azeez ta maka mijin ta mai suna Olushesi dan shekara 45 a kotun Igando dake jihar Legas sanadiyyar kaurace mata da yake yi.
Bilikisu wacce ‘yar kasuwa ce ta roki akotun da ta warware auren ta da mijinta saboda kaurace mata da yake yi da hakan har rashin lafiya yakan sa ta.
” Kwanciyar da nayi na karshe a asibiti kafin na zo kotu likita ya fada min cewa rashin saduwa ne da mijina akai-akai ya kawo mun rashin lafiya.”
Bilkisu ta zargi mijinta da cewa tun da ya yi sabuwar amarya ne ya kaurace mata sannan ya yi watsi da kula da dan su daya namiji da suka haifa.
‘‘Olushesi ya kan lakada mun duka saboda amaryar sa sannan daga ni har dan yaro na bamu tsira daga masifar wannan amarya ba.”
Bayan haka Olushesi y ace tabas ya kaurace wa Bilikisu amma ya yi haka ne saboda ramakon kaurace masa da ta fara yi.
” Ranar da Bilkisu ta fara kaurace mini babu irin juyin duniyan nan da ban yi ba ta amince da ni amma ta ki sai dai ta tashi daga kan gadon ta yi shinfida a kasa ta kwanta.”
Alkalin kotun Akin Akinniyi ya daga ci gaba da shari’ar ranar 12 ga watan Afirilu.