Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, a karkashin jam’iyyar APC, Shehu Sani, ya bayyana cewa tuni, tun bayan samun nasar zaben 2015 daurin tsintsiyar APC ya sakwarkace, yayi laushi ya fara dai-dai cewa.
Sani, ya jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari da ya ceto jam’iyyar daga riftawa cikin wawakeken ramin da babu mai iya fitar da ita.
Ya jinjina wa Shugaban Kasa ne saboda karfin halin da ya nuna ya soke karin wa’adin da aka yi wa shugabannin jam’iyya na kasa, na jihohi da na kananan hukumomi zuwa shekara daya.
A bisa dukkan alamu, kakkausan kalaman da Shehu Sani ya yi dangane da abin da ya kira kasassabar da aka yi aka kara wa shugabannin jama’iyya wa’adi, za a iya cewa sanatan ya firzas da duk wani yawu mai dacin haushin wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar da ya ke ji.
Haka kuma da wuya sanatan ya kara yin irin wadannan zafafan kalamai, domin ya ce komai, ko kuma a ce ya rigaya ya cinye Kasuwar Kantin Kwari, ta Kano, don haka babu wani abin da zai shiga ya saya a Kasuwar Danmagaji ta Zariya.
Shehu Sani ya ce idan jam’iyyar ta ki amfani da shawarar Buhari, to al’amurra za su damalmale wa APC nan gaba. Don haka ya ce da muguwar rawa, gwamma kin tashi.
“Za mu iya cewa Shugaba Buhari ya ceto jam’iyyar daga kusan afkawar da ta yi cikin ramin da babu mai iya ceto ta.
Ya yi namijin kokarin cire kurwar maitar da wasu dibgaggun ‘yan jam’iyya suka dasa domin son ran su kawai.
“ Da farko yaudarar sa aka yi, ya amince da karin wa’adin, amma yanzu kuwa ya je ya yi nazari tsaf, ya gano inda gaskiyar ta ke.
“Ai da mun sake an tafi a cikin karin wa’adi har aka yi zaben-fitar-da-gwani, to matsawar wani dan adawa ya garzaya kotu, za mu iya wayar gari ga zabe ya zo, amma ba mu da dan takarar shugaban kasa, ‘yan takarar gwamnonin jihohi, na sanatoci da na majalisar tarayya. Domin ko da mun tsaida su, to kotu cewa za ta yi haramtattu ne, dama kuma haramtattun ne.”
Sanata Sani ya kara da cewa dama shi da wasu sanatoci sun kalubalanci wannan karin wa’adin da aka yi wa shugabannin APC cikin watan da ya gabata. Kuma ko cikin makon da ya gabata, sai da suka shaida wa shugaban jam’iyya, John Oyegun cewa karin fa haramtacce ne.
“Wato abin da ke faruwa shi ne, akwai wasu gungun ‘yan-ta-kifen da ke yaudarar shugaban kasa da kuma jam’iyya, domin kawai neman biyan bukatar kawunan su. Dalili kenan kowa ya san tun da aka ci zaben 2015 jam’iyyar ta wargaje, hadin kai ya gagara, sabanin yadda aka san APC kafin a ci zabe.”
“Ni fa dama tun da aka yi wannan kasassabar na rika tunanin cewa, wai jam’iyyar da ta rika bin jama’a gida-gida ta na yi musu alkawurran kawo canji da kakkabe duk abin da ake yi ba bisa ka’ida ba, kuma wai aka wayi gari ita ce ta shimfida wannan haramtaccen karin wa’adin da babu shi a cikin dokar jam’iyya ko dokar kasa.”
Sanatan ya kara da cewa duk irin wannan kwamacala ce ta rika taruwa ta na yawa har ta danne jam’iyyar PDP ta kasa tashi.
“Wato akwai wasu a cikin jam’iyyar APC, musamman gwamnoni. A kowace Juma’a bini-bini za ka ga sun wanko riga sun je Sallar Juma’a a Fadar Shugaban Kasa. Su a na su tunanin jam’iyyar ta su ce, su kadai, domin sun fi kowa kusanci da shugaban kasa. Ba su komai sai faman fada da rikici tsakanin su da wadanda suka sadaukar da komai na su domin APC ta kafa gwamnati.
“Tun bayan nasarar zaben 2015, sai daurin tsintsiyar APC ya faske, tsintsiya kuma ta tarwatse. Aka maida wasu mutane irin su Bola Tinubu, Bukola Saraki da sauran su saniyar-ware. Ba wai ina kwance wa junan mu zani a kasuwa ba ne, amma gaskiya ce na ke fada, kuma bayyana ta shi ne mafi dacewa.”