KARIN WA’ADI: Buhari ya yi daidai – Tinubu

0

Babban jigon jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari dangane da kiran da yayi wa uwar jam’iyya ta soke karin wa’adin da aka yi wa shugabannin jam’iyyar.

Da ya ke bayani a cikin wata takardar da aka raba wa manema labarai, kuma ya sa mata hannu da kan sa, Tinubu ci gaba da cewa Buhari ya yi na sa kokarin, ya fadi gaskiya, kuma kai tsaye ba tare da nuku-nuku ba.

“Da Buhari ya ga dama sai ya kyale a tafi a karkace a kan tsarin da aka yi a karin wa’adi ga shugabannin jam’iyya a ranar 27 Ga Fabrairu, amma sai ya nuna shi mutum ne mai matukar ganin ya ja ragamar jam’iyyar nan zuwa ga hanya mikakka.

“Wannan rana abin farin ciki ce ga dukkanin masu so dimokradiyya tabbatacciya ta dore a kasar nan.

Tinubu ya kuma ci gaba da cewa abin da Buhari ya yi, zai kara karfafa jam’iyyar ta hanyar bayar da dama ga mambobin ta, ciki har da wadanda ke kan mulkin jam’iyyar a yanzu su wajen sake tsayawa takara domin su taimaka wa jam’iyyar kamar yadda su ke ganin ya dace.

Don haka sai ya kara da cewa ya kamata jam’iyyar ta hanzarta wajen shirye-shiryen gudanar da gangami da kuma zabukan sabbin shugabanni kamar yadda jadawalin zaben shugabannin jam’iyyar ya gindaya.

Ya ce wannan ba karamar nasara ba ce ga Najeriya baki daya, don haka ya kamata a yi watsi da tsohon salon siyasar dauri, a dauki sabon salo mai kara jaddada dimokradiyya da cikakkiyar dama ga kowa.

Share.

game da Author