Jirgin Arik Air ya yi saukar bazata a Ghana

0

Wani tiririn hayaki da ya tirnike jirgin Arik Air ya haddasa matukan jirgin yin saukar bazata a birnin Accra na Ghana.

Jirgin dai na fasinja ne da ke jigila daga Lagos zuwa Accra, an gani kuma an rika jin kauri da tiririn hayaki da aka hakkake daga cikin injin jirgin ya rika fitowa.

Wani fasinja dai a jiya ya shiga soshiyal midiya ya na korafin irin rashin mutunci da ka yi wa fasinjojinn jirgin a tashar saukar jirage ta Accra, bayan jirgin na Arik Air ya yi saukar bazata.

Sai dai kuma kakakin kamfanin Arik Air, Adebanji Ola, ya ce babu wani abu da aka yi wa fasinjojin domin kowanen su ya fita daga jirgin salum-alum.

Ya kuma tabbatar da saukar gaggawar da jirgin ya yi.

Share.

game da Author