Gwamnatin jihar Oyo ta gano wasu baragurbin asibitoci a garin Ibadan da suke aiki ba tare da lasisi ba.
Gwamnatin ta yi haka ne domin kawar da baragurbin asibitoci dake dawo wa fannin kiwon lafiya hannun agogo baya a jihar.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Azeez Adeduntan yace sun rufe asibitocin bayan sun gano cewa asibitocin na aiki ba tare da takardun izini ba, rashin kwararrun ma’aikata da sauran su.