Jami’ar Maryam Abacha American University dake Nijar (MAAUN) ta sami shiga kungiyar jami’o’in kasa da kasa (IAU).
Jami’ar MAAUN ta sami shiga kungiyar IAU ne bayan ta cika sharadun shiga kungiyar.
Shugaban kungiyar Hilligje Van’t Land ya yabawa jami’ar MAAUN cewa ta cika dukkan sharuddan da ake nema jami’a ta cika don shiga wannan kungiya.
Sannan ya Kara da cewa shigar jami’ar kungiyar zai bata daman gogayya da jami’oi na duniya da samun duk wani gudunmuwa don samun shahara da kuma amincewar da ake bukata a duniya kamar irin takardun dabarun koyarwa na kungiyar, damar shiga kundin ilimin jami’oi na duniya, yadda za a iya gudanar da karatu da samun inganci daga Dalibai da dai sauransu.
A karshe shugaban jami’ar MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo ya yi murna mutuka kan yadda jami’ar ta samu damar shiga wannan kungiya da irin amfanin da jami’ar da daliban jami’ar zasu amfana da shi.
Ya kuma ce nan ba da dadewa ba za su bude rashen jami’ar a jihar Kaduna don koyar da aiyukkan likita da Unguwar Zoma.