Jami’an tsaro sun kama barawon duwatsu a Jigawa

0

Rundunar ‘Civil Defence Corps (NSCDC) a jihar Jigawa ta kama wani matashi mai shekara 25 da satar duwatsun da gwamnati ta tara na wani aikin titi da take yi.

Kakakin rundunar Adamu Shehu ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a Duste ranar Juma’a.

Shehu ya ce ma’aiaktan su sun kama matashin ne yana satar duwatsun ne a daidai suna aikin yawon duba gari.

Matashin ya ce ya saci duwatsun ne don ya karisa ginin da yake yi ganin saura makonni uku a daura masa aure.

Share.

game da Author