Jami’an Hana Sha Da Fataucin Kwayoyi (NDLEA), sun kama wata zungureriyar tirela dankare da lodin maganin codeine maganin tari, har kwalba 24,0000, wanda matasa suka maida kwayar da su ke sha suna buguwa.
An kama babbar motar ne a Katsina, kamar yadda Babbar Kwamandar NDLEA ta Katsina, Maryam Sani ta bayyana wa manema labarai yau Talata a Katsina.
Ta kara da cewa an kama mutane shida masu alaka da safarar maganin daga Anacha.
Ta ce an kama direban motar, wani mai taimaka wa direban ya na tukawa idan ya gaji, da kuma kwandastocin motar su biyu.
Maryam ta ci gaba da cewa sauran wadanda aka kama su ne manajan kamfanin Sunglow Equity Nig. Ltd, wanda ake zargin shi ne mai maganin, da kuma jami’in da ke sayar da kaya a kamfanin.
Gwamnatocin jihohin Arewa su na nuna damuwa da kuma zargin maganin tarin ya na da sanadarin kodin dalili kenan ake shan sa ana buguwa. An ce sinadarin da ke cikin ruwan maganin ya na da alaka da hodar iblis da kuma garin hodar a-ji-garau.
Rahotanni sun nuna cewa yawancin masu sha kwayoyi na amfani da shi idan ba su iya sayen kwayoyin buguwa masu dan Karen tsada.
Har yau dai gwamnatin jihar Katsina ba ta yi wata doka da ta haramta sha da safara da sayar da maganin na tari da mura ba.
An dai kama tirelar cike da maganin ne a unguwar Dutsin-reme a Katsina.
Maryam ta ce za a gurfanar da wadanda aka kama din a gaban shari’a.