INEC TA WANKE KANO: Babu tabbacin cewa yara kanana sun yi zabe a Kano

0

Shugaban Kwamitin da hukumar zabe ta kafa don duba korafe-korafen da akeyi cewa wai yara kanana sun yi zabe a Kano, Abubakar Nahuce ya bayyana wa manema labarai a Kano, cewa binciken su ya nuna cewa ba gaskiya bane cewa da akeyi wai yara kanana sun kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da akayi a Jihar Kano.

” Binciken da muka gudanar tun zuwan mu Kano, bai nuna tabbacin hakan ya faru ba. Mun tattauna da ‘yan jarida, kungiyoyin sa Ido, duk babu wanda ya iya tabbatar mana sahihancin wadannan korafe-korafe.

Idan ba a manta ba, ana zargin hukumar zabe na Jihar Kano cewa ta bari yaran da basu kai yin zabe ba kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da akayi a Jihar.

An yayyada hutuna da bidiyo a shafunan sada zumunta wato Facebook da sauran su.

Share.

game da Author