Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya kaddamar da Kwamitin Sa-ido Kan Harkokin Zabe. An kaddamar da kwamitin ne a matsayin farkon somin-tabin shirye-shiryen zaben 2019.
Da yake kaddamar da kwamitin mai dauke da mutane tara, Farfesa Yakubu ya yi tsinkayen cewa a yadda mu ke da jam’iyyun siyasa 68 da kuma mazabu 1,558, to aikin gudanar da zabe a Najeriya abu ne mai cike da kalubale da yawa.
“A matsayin mu na hukumar zabe, tilas mu bi diddigin duk wani ko wasu tsare-tsaren shirin gudanar da zabe, wanda aka kafa wa kwamitin mutane 16, wanda da kwamitin ne za a rika dogaro. Ya ce su ne kamar sakatarorin da ke gudanar da ayyukan EPP.
“Mun bi a hankali mun zabo maza da mata tare kuma da ‘yan mata da samari wadanda muka tabbatar da cewa su na da sadaukar da kai da hazakar iya dukkan ayyuka da za a ba su domin su yi fiye ma daukar awoyi 24 da kullum.
“A madadin hukumar zabe, ina taya ku murna sosai. Sai dai wannan fa babban aiki ne a kan mu mai cike da kalubale.
Yakubu ya bai wa kwamitin makonni hudu ya kawai masa rahoton aikin.
Mataimaki Na Musamman ga Shugaban INEC, Mohammed Kuna, shi ne shugaban kwamitin, sai sauran mambobi su takwas da za su taya shi aiki.