INEC ta dakatar da ma’aikata 205 saboda harkallar da suka tafka a zaben 2015

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta dakatar da jami’an ta har 205 saboda hannun da bincike ya tabbatar sun a da shi a harkallar zaben 2015.

Shugaban Hukumar, Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yayin da ya ke jawabi a taron Kunyigar Sa-ido a yau Talata a Abuja.

Ya ce wannan ne karo na farko da INEC ta taba yin irin wannan gagarimin kokarin ladaftarwa, a bisa ka’idar da ke shimfide a cikin dokokin hukumar da ke magana a kan ladabtarwa.

Mahmud ya ce soke-soken masu ma’ana da jama’a suka rika yi, sun taimaka wa hukumar wajen gudanar da ayyuka da suka hada har da gudanar da sahihin zabuka.

Ya ce tuni jami’an hukumar su na wurare daban-daban su na gudanar da ayyukan shirye-shiryen zaben 2019.
“Bukatar mu shi ne mu doka ma’aikata nagari a matsayin jami’an gudanar da zaben 2019, ba za mu amince da baragurbi ba.

“ Sahihancin zabe ya dogara ne ga irin sahihan mutanen da aka dora domin su gudanar da ayyukan zaben.

“Kwamitin ladaftarwar dai ya amince da a dakatar da jami’an su 205 saboda rawar da suka taka a zaben 2015, kuma wannan ne karon farko da aka fi ladaftar da jami’ai masu yawa a tarihin kafa hukumar.

“Muna da ma’aikata masu kishi sosai, amma hakan ba zai hana ko ma wa aka kama da laifi a ki hukunta shi ba. INEC ta na aikin ta ba sani ba sabo ne.

Ya ce jihohin Rivers, Anambara, Delta, Lagos, Cross-River, Osun, Enugu, Kano da Filato ne aka fi yin rajista da yawa.

Daga nan sai ya kara da cewa hukumar sa ta gudanar da zabuka har 179 daga hawan sa zuwa yau, amma guda biyar ne kadai aka garzaya kotu a kan su.

Ya ce hakan kuwa ya na nuni ne da irin yadda hukumar ta sa ke gudanar da sahihin zabe.

Daga nan sai ya ce hukumar sa ta sake karbar bukatu har guda 100 na kungiyoyin da ke so a yi musu rajistar jam’iyya, amma guda tara ne kadai suka cika sharudda.

Don haka ya ce za ta iya yiwuwa jam’iyyu 80 ne za su fafata zaben 2019.

Daga nan sai ya kara jadda cewa zaben 2019 sai ya fi na 2015 sahihanci.

Share.

game da Author