Tsohon gwamnan jihar Nasarawa Adamu Abdullahi ya karyata cewa da akayi a majalisa wai yana kitsa makarkashiyar tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
Idan ba a manta ba An zargi Sanata Abdullahi Adamu da kitsa makarkashiyar tsige Shugaban Majalisar, Sanata Bukola Saraki.
Sanata Obinna Ogba daga jihar Ebonyi ne ya yi wannan zargin tare da cewa ya na da kwararan hujjoji.
“Na tashi yau da safe domin na sanar da Majalisa wata makarkashiya da su Sanata Abdullahi Adamu ke yi na tsige Shugaban Majalisa. Kuma idan ba ku manta ba, cikin watan Janairu Sanata Misau ya ce wasu na kulla makarkashiyar tsige Sanata Saraki daga shugabanci.” Obinna yace.
Sai dai a martani da ya maida, Sanata Adamu ya ce ” Bukola da ne a waje na sannan ban taba nuna son zama shugaban majalisa ba wanda ina da damar yin hakan a matsayi na sanata. Wannan shiri ne kawai don a ci mini mutunci wanda ba zai yiwu ba ko da ana so.
” Ace wai sai yanzu ne da an buga gangar siyasa shine zan ce wai a tsige shugaban majalisa. Kuma kamar yadda na fadi cewa Saraki kamar da ne gareni, a ganina babu ribar da za aci idan har ma hakan za ayi. Wannan batu bata , sharri ce akeyi mini sannan a shirye nike domin in tsaya a gaban kwamitin da’a na majalisar.
” Ka ga a nan yar fara ta nuna. Sai ya kawo wadannan shaidu da yake cewa wai yana dasu kowa ya gani.”