Hukumar Kwastam ta kama tankar mai dankare da shikafa a Sokoto

0

Shugaban hukumar kwastam dake kula da shiyar Sokoto, Kebbi da Zamfara Nasir Ahmed ya bayyana cewa sun kama babbar motar mai cike makil da buhunan shinkafa a jihar Sokoto.

Ya sanar da haka ne ranar Juma’a da yake zantawa da manema labarai a Sokoto.

Ahmed ya ce sun kama tankin man ne a hanyar Sokoto zuwa Illela inda suka tsamo buhunan shinkafan 460 jike da bakin mai.

” Saka shinkafar da suka yi a cikin bakin mai ya lalata shinkafar, sannan an kiyasta kudin buhunanshinkafar za su kai naira miliyan 7.8.”

Ya roki mutane da su hada kai da ma’aiakatan hukumar domin ganin an kau da masu fasakwauri a iyakokin jihar.

Share.

game da Author