Hukumar Kula da Alkalai ta Kasa, NJC, ta nemi a yi wa wasu manyan alkalan kasar nan biyu ritayar dole.
Manyan alkalan su ne Theresa Uzokwe, Cif Joji ta Jihar Abia da kuma Obisike Oji, na Babbar Kotun Jihar Abia.
Hukumar ta ce ta yanke shawarar a yi musu ritaya ne bayan ta yi nazarin kwamitoci biyu da aka kafa domin su binciki wata barankyankyama da alkalan suka tafka.
Cikin wata takarda da kakakin hukumar Soji Oye ya sa wa hannu, NJC ta kuma yi kakkausan gargadi ga Mai Shari’a S.E Aladetoyinbo da Olusola Ajinike Williams na Babbabr kotun Abuja da Lagos.
Hukumar ta kuma kafa wani kwamitin da zai binciki wasu alkalan Kotun Koli ta Tarayya guda biyu.