HARIN GIDAN SHEHU SANI: Za a dabdale a Kotu, Inji Lauyan Uba Sani

0

Mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna kan harkar Siyasa da al’amurran gwamnati, Uba Sani ya yi tir da wata kara da aka shigar ana zargin sa wai ya tura wasu yan ta’adda su far wa gidan sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, inda har wai an ji ma wasu rauni sannan an sace kaya masu tsada.

A wani kara da aka saurara a kotun dake unguwar Barnawa Kaduna, an gurfanar da wani matashi dan shekara 22 mai suna Adamu Abdullahi a gaban alkali inda bayyana cewa Uba Sani ne ya tura su wannan gida domin su far wa iyalan gida.

Ko da yake wannan bayanai na kunshe ne a takardar da ‘yan sanda suka mika a gaban alkalin, wannan matashi ya ce shi bai aikata hakan ba.

Uba Sani ya karyata wannan zargi da ake masa, sannan yace ko sanin wannan matashi bai yi ba.

Lauyan Uba, Barr Mohammed Abdul-Rauf ya ce ba za su nade hannu su bari wannan abu ya wuce haka kawai ba domin cin mutunci ne sannan akwai cin fuska a cikin sa.

“ Za mu daukaka kara sosai sannan za mu nemi a biya mu kudade don cin fuskar da akayi mana.

“ Idan ka duba korafin da aka mika gaban kotu, zaka ga sam babu wani abu da zai nuna wai an kai wa gidan Sanata Sani, hari. Wannan wani abu ne kawai akayi don a ci wa Uba Sani Mutunci wanda baza mu bari haka nan ba.

“ Mun kammala shiri tsaf domin shigar da kara babban kotu don a nema mana hakkin mu” Inji Abdul-Rauf.

Share.

game da Author