Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce har yanzu jam’iyyar APC ba ta da farin jini a yankin Kudu-maso-gabas.
Ya bayyana cewa ba da dadewa ba za a yi zaben kananan hukumomi a jihar.
Shekaru shida kenan Okorocha ke ta yin alkawarin gudanar da zaben kananan hukumomi amma ya na daga zaben.
Ya yi kira ga majalisar jihar Imo su gaggauta fito da dokar kananan hukumomi, yadda za a yi zabe a cikin watan Mayu.
Gwamnan ya ce jam’iyyar APC ba ta da farin jini a jihohin Kudu-maso-gabas, amma za su yi kokari su karfafa tasirin jam’iyyar ta hanyar kara wa kamfen na Shugaba Muhammadu Buhari tasiri sosai a yankin.
Yayin da ya ce za su goya wa Buhari baya a zaben 2019, ya kuma kalubalanci masu sukar surikin sa, Uche Nwosu da ya tsaida a matsayin dan takarar gwamnan jihar.
“Wadanda ke jayayya da tsaida Uche Nwosu takarar gwamna, ni ban ga abin tada jijiyar wuya ba. Ai ban hana kowa tsayawa ba. Idan ku na da dan takara sai ku kawo na ku ‘yan takarar, a yi zaben fidda gwani a tantance.
Discussion about this post